Waye Michael Saylor?
An haifi Michael saylor a birnin Lincoln dake jihar Nebraska dake Amurka a 1965 (shekaru 60 dai dai), family dinsa mafiya yawan su sojojin sama ne. Sai dai shi bai zama Soja ba.
Yayi degree na farko a fagen Aeronautics and Astronautics Technology. A wata makaranta dake jihar Massachusetts, wato Massachusetts Institute of Technology a America.
Ya kafa kamfanin Micro strategy a shekarar 1989 (shekaru 36 da suka wuce) lokacin yana da shekaru 24 a duniya. An kafa kamfanin da nufin yin Business Intelligence. Kuma abinda kamfanin ya shahara dashi kenan daga 1989 har zuwa 2020.
Dama tuntuni kamfanin yana harkar Stock, suna da MSTR share nasu. Daga cikin hanyoyin da suke samun kudin kudin sayan Bitcoin akwai Stock market ta hanyar MSTR share dinsu.
Kamfanin Micro strategy (kafin 2020) yana harkar siyar da Business Intelligence Software ne (BI), amma ga manyan kamfanoni na duniya. Daga bisani a 2020 suka canza harkar ko ma suka dakatar da siyar da Business Software.
Bincike ya nuna Micro strategy suna harkar Business Software har yanzu sai dai ta wata fuska daban tare da wasu kamfanoni.
Software masu matukar girman gaske da suke saida wa kamfanoni domin Internal Data dinsu.
A watan August na 2020 sai kamfanin ya koma harkar Bitcoin Business Intelligence (BBI) wanda suke sayan Bitcoin daga kudaden da suke samu ta hanyar riba da aron kudi da suke karba. A yanzu haka Micro strategy suna da Bitcoin guda dubu dari 650,000 wadanda suka zarce Dala biliyan 55 a farashin Bitcoin a yau (87,000 USDT).
Primary Reserve Asset na kamfanin shine Bitcoin, basa ajiye Dala, Gold ko Silver. Bitcoin kawai suke saya a bisa tsarin Holding indefinitely.
Su waye ke da wannan Bitcoin?
Dukkan wadanda suke da hannun jari (share holders) a Micro strategy su suke da wadannan Bitcoins da Micheal Saylor yake saya. Sai dai shi Michael saylor shi yake da largest share a kamfanin.
Daga cikin aikin Bitcoin Business Intelligence da Micro strategy suke yi shine; suna karban kudin manyan mutane, manyan kamfanoni da kasashe suna sayan Bitcoin a spot market suna rike musu, suna holding musu. Suna karban kudi akan kowane Bitcoin kwaya daya a kowace rana.
Akwai kasashen da suke bayar da kudi wa Micro strategy su saya Bitcoin su ajiye musu, wannan ajiyar da Micro strategy suke yi na daga cikin hanyoyin samun kudin Kamfanin a yau.
Michael saylor mutum ne da wadanda suka san shi suka ce mai wadaka da fantamawa sosai.
Ance suna da gidaje a Ohio, Florida da New York wanda kowanne ya haura Dala miliyan 30.
Kamfanin Micro strategy suna samun manyan kudade ta hanyar Bitcoin Sofware services da suke yi, da kuma Bitcoin Orange Decentralized ID, da Bitcoin Monetization Services.
Micro strategy suna ajiye Bitcoin dinsu a Cold wallets, sai dai su suka kirki wannan cold wallet din, anyi ta neman su fitar da ita su siyar ma duniya sunki.
Duk da haka, duk bayan kwana 25 ko 40 suna canza cold wallet din da suke rike da Bitcoins dinsu zuwa wasu sabbin wallet.
Kamfanin Micro strategy yana daga cikin kamfanonin da suke da kwararrun masu bincike a duniya akan Bitcoin market.
Sannan Micro strategy suna raising kudade ta hanyar Bond idan gwamnati zata yi, kamar a US da England. Suna kuma bayar da rance suna kuma karba tare da leverage sosai. So, duk Bitcoins din da suke wallets na kamfanin Micro strategy ba na Micheal Saylor kadai ne ba, na kamfani ne.
Sai dai shima yana sayan Bitcoin (personally) yana ajiyewa. Sai dai wannan kuma personal life dinsa ne ba lallai asan hakikanin yawan abinda yake dasu ba.
